Wata Kotu Ta Umarci Ado gwanja Ya Dawo Da Motar Ya Tafi Yin Dani Bai Dawo Ba.

Spread the love

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a unguwar Jaba Kano, ta umarci Mawakinnan Ado Gwanja, ya dawo da motar da ya tafi yin Dani tsawon makomni Uku bai dawo ba.

Ado Gwanja, ya siyi motar ce a Hannun Mai kara , Mustapha Adamu , Amma Gwanjan ya Yi Zargin cewa motar Bata da lafiya, Inda aka umarci Mustapha, ya gyara masa , kuma bayan ya Gyara ne , kotun ta ba wa Ado Gwanja, don ya Yi gwaji , sai Ake Zargin yaki dawo wa da motar tsawon lokaci.

Mai karar ya shaida wa kotun cewar Yana bin Gwanja sauran kudi kimanin naira Dubu 500,000 shi yasa ya Yi kararsa.

A zaman kotun da ya gabata lauyan Mai karar ya roki Kotun, ta bayar da umarnin kamo Ado Gwanja.

Alkalin kotun Mai shari’a Malam Rabi’u Yahaya, ya umarci, Ado Gwanja, ya dawo da motar a ranar 12 ga watan Disamba 2024, Inda kotun ta ce zata juyar da Shari’ar zuwa babbar kotun shari’ar addinin musulinci ta Sabongari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *