Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Gama PRP Kano, ta yanke wa wasu matasa hukunci sakamakon samun su da aikata laifukan hada baki da fasa shago da kuma yin sata.
Laifukan da ake tuhumar su da aikata wa sun saba da sashi na 120, 216 da 133 na kundin SPCL .
Tun a ranar 6 ga watan Disambar 2023 , wani mai suna Auwaal Nasir , yaje ofishin yan sanda na Badawa ya yi korafin matasan da suka hada da Kazim Ibrahim da ake yi wa lakabi da Boka, Muhammed Aliya da ake kira Arne da kuma Ammar Jibrin mai lakabin Ajebo dukkan su mazauna unguwar Badawa.
Ana zarginsu da satar kaya a shago da wayar hannu kirar Iphone 6 mai kimar kudi naira dubu dari da talatin, Azurfofi masu kimar kudi naira dubu dari da tamanin da hudu da kudi naira dubu dari da ashirin da biyar da biyar
Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala ya karanto mu su kunshin tuhumar da ake yi mu su , inda suka amsa cewar sun aikata laifin.
Kotun ta tambayi mai gabatar da kara , ko wadanda ake tuhumar sun taba aikata laifi, nan ta ke ya ce tabbas, wanda ake tuhuma na daya an taba kama shi da laifin satar mota , har aka kai shi sashin binciken manyam laifuka na jahar Kano daganan aka gurfanar da shi a gaban kotun Majistiri.
Ya yin da na biyu da na uku kuma sun addabi mutanen unguwarsu har suke yawan korafi akan su.
Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya yanke mu su hukuncin daurin watanni shida a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya a laifi na farko, ko biyan Naira dubu goma-goma kowannen su.
A laifi na biyu na fasa shago kotun ta yanke mu su hukuncin daurin watanni uku-uku ba tare da zabin biyan tara ba .
Sai laifi yin sata kotun ta yanke mu su hukuncin daurin shekara daya kowannen su, ko zabin biyan tarar Naira dubu Talatin-Talatin.
A karshe kotun ta yi umarnin su biya mai kara kudin sa Naira dubu dari uku da hamsin da bakwai da dari biyar.
Idongari.ng