Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta , a unguwar Kwana hudu Kano , ta yanke wa wasu matasa biyu hukuncin daurin watanni 21, sakamakon samun su da aikata laifuka 4.
Ana zargin Shamsu Ahmed mai shekaru 26 da Zailani Ya’u mai shekaru 27 da hada kai wajen aikata laifi, samun su da Makami, shiga ta laifi da yin sata, wanda yin hakan ya saba da sashi na 120, 264, 313,133 na kundin SPCL.
Idongari.ng, ya ruwaito cewar matasan sun shiga gidan wani babban lauya , a jahar Kano mai suna Abubakar Balarabe Mohd ( SAN), inda suka sace masa Batiran sola guda biyu ma su kimar kudi naira dubu dari , da kuma wani Inji mai kimar kudi naira dubu dari biyu.
Matasan sun yi kokarin guduwa a lokacin da suka ga jami’an yan sanda suna gudanar da bincike , inda suka cafke su tare da gurfanar da su a gaban kotun kamar yadda idongari.ng, ya ruwaito .
Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala, ya karanto mu su kunshin tuhumar da ake yi mu su, inda nan ta ke suka amsa laifin su.
Alkalin kotun mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya yanke mu su hukuncin daurin watanni 4 kowannen su a laifin hada kai , ko zabin biyar tarar naira dubu biyar.
Yayin da laifin samun su da zabgegiyar wuka kuma daurin watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba.
A laifin shiga ta laifi an daure su watanni 6 babu zabin biyan tara.
Sai laifin sata daurin watanni 5 da kuma Bulala 60 kowannen su.