Wata kotu ta yanke wa matashin da yan sandan Kano suka gurfanar hukunci, bisa samun sa da Danbuda a kugunsa

Spread the love

Kotun shari’ar addinin muslinci dake zaman ta a unguwar Gama Kano, ta yankewa wani matashi mai suna Isma’il Umar, hukuncin daurin watanni biyu a gidan a jiya da gyaran gali da tarbiya, sakamakon samun sa da Danbuda guda biyu.

Tunda fari dai jami’an yan sandan Kano ne, suka kama shi a lokacin da suke aikin sintiri , sannan suka gurfanar da shi a gaban kotun.

Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa, inda nan ta ke ya amsa laifin.

Sai dai wanda ake tuhumar ya shaida wa kotun cewar, wajen Gangi zaije da Danbudan da aka samu a kugunsa.

Mai gabatar da karar ya roki kotun ta yanke masa hukinci, bisa ikirarin bakinsa.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya yanke masa hukuncin daurin watanni biyu ba tare da zabin biyan tara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *