Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a Unguwar Gama Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin daurin shekaru biyu, da kuma yi masa bulala arba’in, sakamakon samunsa da aikata laifukan sata.
Tunda fari an gurfanar da matashin mai Suna Sahabi Abdulkarim, dauke da tuhume-tuhume guda 6, da suka hada da shiga ta laifi, fasa Shago da kuma aikata satar kayan mutanen Fanisau da Jaba a Kano.
Mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa, inda ya amsa uku sannan ya musanta uku.
Kan hakan ne mai gabatar da karar ya roki kotu, ta bashi rantsuwa kan kunshin takaddun da ya musanta, kuma kotun ta amince da bashi rantsuwar.
Sai dai sauran laifuka ukun da ya amsa na shiga ta laifi, fasa Shaguna da sata, kotun ta yi masa daurin shekaru biyu a gidan ajiya da gyaran hali sa tarbiya tare da yi masa bulala arba’in.
- Shugaban Senegal mafi ƙarancin shekaru ya sha rantsuwar kama aiki
- Farashin Kayayyakin Masarufi Na Ci gaba Da Tashi A Najeriya