Wata Kotu Ta Yanke wa Mutumin Da Ya Ke Tura Fina-finan Batsa Tare Da Yi Wa Matar Aure Dan Kira Hukunci A Kano.

Spread the love

Kotun shari’ar addinin musulinci mai namba 2, dake zaman ta a kofar kudu gidan sarki, ta yanke wani matashi hukuncin daurin watanni shida a gidan gyaran hali da tarbiya sakamakon samun sa da laifin lallashin Matar aure.

Mutumin mai suna Inusa Adamu Idris, mai shekaru 36, Mazaunin Unguwar Kawo a jahar Kano.

An gurfanar da shi bisa zargin lallashin Matar aure, Wanda hakan ya Saba wa sashi na 389 na kundin penel code.

Mai gabatar da Kara, Detective Aliyu Abideen, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake Yi masa inda nan ta ke ya amsa laifinsa, kan cewar tabbas ya na lallashin Matar aure ta hanyar tura Mata fina-finan batsa da yake Yi , tare da sanya ta a wani group da ake dora fina-finan batsa.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa, Mutumin ya samu nambar Matar ce , bayan ta Kai masa gyaran kekekn dinki da ya ke Yi Mata.

Matar auren ta Fara sanar da Mijin ta kan kalaman batsa da kuma fina-finan da ya ke turo Mata, Wanda daga bisa miji ya garzaya sashin binciken manyan laifuka na yan sanda, inda aka ka moshi.

Bayan ya amsa laifinsa, mai gabatar da Kara Aliyu Abideen, ya Yi roko karkashin sashi na 350 da 356 karamin kashi na biyu na kundin ACJL 2019, tare da Neman alfarmar kotun ta yanke masa hukuncin nan ta ke, tunda bai musanta zargin da ake Yi ma sa ba.

Alkalin kotun mai Shari’a, Isah Rabi’u Gaya, ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida, a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya ko zabin biyan tarar naira dubu talatin ga gwamnatin jahar Kano.

Kotun taja hankalinsa tare da Yi masa iyaka da Matar auren bayan an goge dukkanin abubuwan da ya tura Mata.

An kuma cike mu su form na zaman lafiya bashi ba Matar magidancin da ya kawo korafin har tsawon shekaru 10, ba tare da wani ya ci zarafin wani ba.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa kotun ta bayar da umarnin tura shi zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya, matukar bai biya tarar ga gwamnatin jahar Kano ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *