Kotun shari’ar addinin musulinci dake zamanta a unguwar Gama PRP Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin daurin watanni shida a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya sakamakon samunsa da aikata laifin cuta ta hanyar damfarar al’umma.
Tunda farko ana zargin matashin mai suna Nuraddin Rabi’u Muhd mazaunin Zariyan jahar Kaduna, da laifin karbar Katin wayar Salula na MTN da Aitel, a wajen wani mai suna Abubakar Musa Danzaki, na naira dubu saba’in, a ranar 31 ga watan Maris 2024.
Bayan matashin ya biya kudin ya tafi, sai suka koma Ganyen Zogale, inda mai sana’ar siyar da katin wayar ya nemi taimakon jama’a har aka samu nasarar kama shi kamar yadda jaridar Idongari.ng ta ruwiato.
Laifin da ake zarginsa da aikata wa ya saba da shashi na 2026 na kundin SPCL.
Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa inda nan ta ke ya amsa laifinsa.
Mai gabatar da kara ya yi roko karkashin sashi na 350, da kotun ta yanke masa hukuncin nan ta ke tunda ya amsa laifinsa.
Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida ba tare da zabin biyan tara ba, sannan kuma zai biya wadanda ya cuta kudinsu da kuma wahalhalun da suka yi.
- An rufe kantin China kan zargin nuna wa ƴan Najeriya wariya
- Najeriya ba ta kai lokacin kafa ƴan sandan jihohi ba – Spetan Ƴan sanda
A wani Labarin kuma, an sake karanto masa kunshin tuhumar tuhumar cutar wani mai sana’ar siyar da katin waya har naira dubu 177, a yankin unguwar Mariri Kano, inda ya karbi katin waya sannan ya biyashi amma sun koma ganyen Zogale da wasu takaddu
Bayan karanto masa kunshin tuhumar ya amsa laifinsa , sai dai sakamakon kurewar lokacin alkalin kotun ya sanya ranar 19 ga watan Mayun 2024, don yi masa hukunci kan tuhuma ta biyu da ake yi masa.