Wata kotun addinin musulinci ta yi umarnin tsare yan matan da ake zarginsu da bata budurwa a Kano

Spread the love

An gurfanar da wasu yan mata uku agaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Gama PRP yankin karamar hukumar Nasarawa Kano, bisa zarginsu da hada baki, aikata laifi, tsoratarwa da kuma bata suna.

Laifin da ya ci karo da sashi na 120, 227 da 198 na kundin SPCL.

Wadanda ake zargin sun hada da , Amina Dahiru, Sadiya Abdullahi da kuma Fiddausi Yahaya.

Tun farko wata mai suna Fiddausi Salisu, ce taje wajen jami’an yan sanda ta gabatar da kara, da cewar yan matan sun bata mata suna da tsoratarwa bayan daya daga cikin yan matan da aka gurfanar da ta rasa wayarta har suka zargeta da cewar ita ce ta dauke mata wayar salular.

Hakan ya sanya su tilasta mata tafiya da ita har zuwa gidansu cikin dakinsu, kuma sun bincika ko’ina ba su ga wayar ba.

Sai dai duk da haka sun jefe ta da muggan kalamai marasa dadi , tare da yada ta a cikin al’umma.

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

Kotu ta aike da yar Tiktok Ramlat Princess gidan gyaran hali bisa zargin yada badala

Bayan gurfanar da su a gaban kotun, mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala ya karanto mu su kunshin tuhumar da ake yi mu su , inda suka musanta zargin.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed , ya aike da su zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya , sakamakon musanta zargin da suka yi, aka kuma dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Janairu 2024 dan gabatar da shaidu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *