Wata Kotun Majistire ta tsare shugaban karamar hukuma da mutane 11, kan zargin hada kai, sacewa da kisan kan Dagaci.

Spread the love

Wata kotun majistare a jahar Katsina ta tsare shugaban karamar hukumar Batagarawa ta jihar, Hon. Bala Garba, bisa zarginsa da aikata laifin hada kai, sace Dagaci da kuma kashe shi.

An gurfanar da shugaban karamar hukumar tare wasu mutane 11 a gaban kotun , kan zargin kisan Dagacin kauyen Dabaibayawa, Alhaji Dikko Ahmad.

Laifin da ake tuhumarsu da aikata wa ya saba da sashe na 59, 249 da 189 na dokar hukunta manyan laifuka ta Katsina.

Bayan gurfanar da su , mai shari’a , Abdulkarim Umar, ya bada umarnin tsare su , a gidan gyaran hali da tarbiya har zuwa ranarĀ  7 ga Maris 2024.

ISYAKU.COM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *