Wata kotun majistiri ta tsare wasu yan mata da mutum 1 kan zargin satar gwala-gwalai N6.8m , a uguwar Sharada Kano

Spread the love

Wata kotun majistiri mai namba 54, dake zaman ta a unguwar Norman’Sland Kano, ta tsare wasu mutane uku da ake zargi da laifin hada kai, shiga ta laifi, sata da kuma siyan kayan sata , wanda laifin ya saba ya saba wa na 97, 343, 287 da kuma na 281 na kundin penal code.

Tun a ranar 15 ga watan Janairun 2024, ake zargin wata mai suna Amira Dayyabu mai shekaru 18 da kuma Asiya Usman mai shekau 16, dukkan su mazauna Garin Rantan a karamar hukumar Bebeji Kano, inda suka shiga gidan wani Alhaji Mujitapha Isah a unguwar Sharada , suka sace mada Gwala-Gwalai masu kimar kudi naira miliyan shida da dubu dari takwas.

Wadanda su ka siyar wa da Muhammed Abdullahi, kan kudi naira dubu dari uku da hansin, shi kuma ya sassara su ya siyar.

Jami’an yan sandan jahar Kano  ne suka samu nasarar cafkesu , bayan sun koma wani gida a unguwar sharadan domin aikata satar.

Idongari.ng ya ruwaito cewa, na’urar CCTV Cemera ta hasko fuskar wadda ake zargi ta farko , lokacin za ta shiga gidan da ta sato gwala-gwalan har zuwa lokacin da ta fito, inda yan sandan suka gurfanar da su a gaban kotun.

Mai gabatar da kara, ya karanto mu su kunshin tuhumar da ake yi mu su na hadakai, shiga ta laifi, sata da siyan kayan sata.

Wadda ake tuhuma ta farko Amira Dayyabu ta amsa laifuka uku na hada kai, shiga ta laifi a kuma yin sata, ya yin da Asiya Usman, ta amsa laifin sata.

Sai wanda ake tuhuma na uku Muhammed Abdullahi, ya musanta zargin siyan kayan sata da siyar da kayan satar ga wani mai suna Abba, da yan sanda ke nema sakamakon guduwa da ya yi.

Lauyan dake kare wanda ake tuhuma na uku ya roki kotun ta bayar da belinsa , sai dai mai gabatar da kara ya yi suka kan rokon.

Mai shari’a Ibrahim Mansur Yola, ya amince da rokon lauyan wanda ake tuhuma na uku, inda ya sanya shi a hannun beli, kan kudi naira miliyan biyar da mutane biyu da za su tsaya masa kuma kowannen zai ajiye naira miliyan uku da hotunan su duba da kimar kudin da aka salwantar.

Kotun ta sanya ranar 15 ga watan Janairu 2024, dan ci gaba da sauraren shari’ar, tare da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *