Wata kotun Majistiri ta yanke wa mutane 2 hukunci ciki harda mai shekaru 82 bisa laifin hadin kai, ta’ammali da kwayoyi a Kano

Spread the love

Kotun Majistiri mai namba 90 dake zamanta a karamar hukumar Madobi Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Haj. Nadiya Ado Saleh ta yankenwa wasu mutane biyu hukunci, bisa samum da aikata laifin hadin kai, ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Mutanen sun hada Iliyasu Idris mai shekaru 82 da kuma Yakubu Dalhatu.

Yan canji a Abuja za su rufe kasuwar canji har sai abin da hali ya yi
Yan bindiga sun sake sace wasu ‘yan mata ‘yan gida daya a Abuja

Mai gabatar da kara ya karanto mu su kunshin tuhumar da ake yi mu su, wadanda suka amsa laifin ba tare da sun wahalar da kansu ba.

Mai shari’ar ta yanke wa Iliyasu Idirs mai shekaru 82, hukuncin daurin sati uku babu zabin biyan tara sakamakon tsufansa, sai dai kotun ta ce , zai biya naira dubu 50,000. idan ya gaza biya zai kara shafe watanni shida a gidan gyaran hali da tarbiya.

Haka zalika mai shari’a ta yanke wa , abokin huldarsa hukuncin daurin shekara daya babu zabin biyan tara, da kuma naira dubu hamsin ko zaman gidan yari na watanni shida.

A karshe mai shari’a Nadiya Saleh , ta wannan ba shi ne karon farko da jami’an taro suka gurfanar da su , a gaban kotu ba, shi yasa ta hana su zabin biyan tarar don su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *