Wata kotun majistiri a jahar Nasarawa ta ce wajibi ne Dauda Rarara ya bayyana a gaban ta.

Spread the love

Kotun Majistiri mai Namba 1 ,dake zaman ta a lafiyan jahar Nasarawa , ta bada umarni ga mawakin siyasar nan na Arewacin Nijeriya Dauda Adamu Abdullahi kahutu (Rarara) , ya bayyana a gaban ta, bisa zarginsa da tayar da hankalin wani mutum mai suna Alhaji Sani Ahmed Zangina .
Mai karar ya zargi Rarara da furta wasu kalamai marasa dadi ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda kalaman suka tayar masa da hankali kamar yadda idongari.ng, ya ruwaito.
A zaman kotun na ranar laraba, lauyan mai kara Barista Isah Nalaraba, ya roki kotun ta bayar da umarnin kamo wanda aka yi karar , sakamakon rashin bayyanarsa agaban kotun.
Lauyan wanda aka yi kara, Barista A. I. Ma’aji, ya roki kotun ta yi watsi da rokon masu karar.
Barista A. Ma’aji ya gabatar wa da kotun wata takadda dake bayyana cewar kotun bata da hurumin sauraren shari’ar.
Sai dai mai Shari’a Maryam Nadabo, taki amince wa da rokon lauyan mai karar na a kamo mawakin Rarara saboda rashin bayyanar sa a gaban kotun, amma ta ce wajibi ne ya bayyana a gaban ta a zama na gaba.
Haka zalika kotun ta yi watsi da rokon da lauyan Rarara dan ta kori karar saboda rashin hurumi har sai wanda aka yi karar ya bayyana a gaban ta.
Mai shari’a Maryam Nadabo ta dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Fabarairun 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *