An gurfanar da wani matashi a gaban kotun shari’ar addinin musulinci A Unguwar Gama PRP , dake jahar Kano bisa zarginsa da aikata laifin haura gida da kuma yin sata, laifin da ake tuhumar da aikata wa ya saba da sashi na 213 da 133 .
Ana zargin matashin mai suna Abubakar Umar , da sace wayar hannu kirar Tecno Spark 16, mai kimar kudi naira dubu chasa’in da takwas , mallakar wani mai suna Yakubu Muhammad.
Bayan mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala , ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa ya musanta zargin.
Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Disamba 2023, don ba wa matashin rantsuwar kore tuhuma sakamakon masu gabatar da kara ba su da wata shaida da za su gabatar wa kotun.