Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zamanta a Shahuci Kano, ta umarci mataimakin sufeton yan Nijeriya , dake kula da shiya ta daya Kano, ya kamo mata wani jami’in dan sanda mai mukamin Insfekta bisa zarginsa da raina kotu.
A baya kotun ta bayar da umarnin dan sandan ya bayyana a gaban ta amma yaki zuwa.
Wani mai suna Alhaji Sa’idu Abdullahi, shi ne ya garzaya gaban kotun domin ta karbar masa hakkinsa , inda ya zargi Insfektan mai suna Abba Shariff, da siyar masa da wani fili a unguwar Hotoro kan kudi naira naira miliyan biyu.
Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Buƙatar Mawaƙi Kan Hana BBC Amfani Da Kiɗansa
An tsananta tsaro a wasu ƙananan hukumomin Kaduna saboda zaɓe
Sai dai mai karar ya shaida wa kotun cewa takaddun filin da aka bashi na bogi.
Mai shari’a Mallam Abdu Abdullahi Waiya , ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Janairun 2024.