Kungiyar Arewa Social Contract Initiative ta yi kira ga Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da ya bar jihar domin wanzar da zaman lafiya a jihar.
Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Sani M. Darma ne ya yi wannan kira a ranar Lahadi a wani taron manema labarai a Kano.
Darma ya bayyana cewa dawowar Aminu Bayero Kano da yunkurin kwato masa mukaminsa zai iya haifar da tashin hankali, rudani da rikici a jihar.
Ya kuma kara da cewa ko da Aminu Ado Bayero na son ya karbi karagar mulkin kano, da sai ya ci gaba da zama a wata jiha kuma ya bi tsarin da ya dace.
“Abin takaici ne a ce bayan sauke Alhaji Aminu Ado Bayero daga karagar mulki, ya amince da tsige shi, ya kuma mika dukkanin kayan sarauta , amma wasu daga gwamantin tarrayya suka zuga shi ya dawo Kano domin a mayar masa da mukaminsa”. Inji Darma.
- Zanga-Zangar Neman Dawo Da Aminu Bayero Karagar Mulki Ta Ɓarke A Kano
- Sarakunan arewacin Najeriya sun nuna damuwa kan halin da ake ciki a Kano
Kadaaura24