Hukumar agajin gaggawa ta sanar cewa matar da ba a bayyana sunanta ba tana jiran shiga motar bas ne a tashar Onipanu Bus Stop a lokacin da ba zato ba tsammani ta shiga naƙuda a ranar Litinin.
Mata ƴan kasuwa ne suka taimaka ma ta, yayin da masu ba da agajin gaggawa suka garzaya wurin.
Hukumar agajin gaggawa ta ƙara da cewa, ta haifi ɗa namiji, kuma tuni aka kai mahaifiyar da yaron asibiti. domin duba lafiyarsu
Babu wani ƙarin bayani da aka bayar game da su baya ga haka, amma ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta na ta wallafa sakonnin taya murna har ma da shawaran sunayen da za a raɗawa jaririn.
Hukumar kwastam ta Najeriya za ta raba kayan abincin da aka kama a faɗin ƙasar