Wata Sabuwa: Iyayen Abba Dan-Kuda Sun Tabbatar Cewa Yana Aikata Daba Da Shan Miyagun Kwayoyi

Spread the love

Iyayen matashin nan mai suna Abba Garba ( Dan Kuda) , da ake zargi da aikata laifin kisan Kai , a yankin Unguwar Panshekara Kano, sun tabbatar da cewar yana harkar Daba da shan miyagun kwayoyi.

Iyayen Abba, sun bayyana hakan ne, ga Kwamishinan Yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, a Wata gayyatar ba zata da yi mu su, domin gana wa da su kan halayyar dan na su.

Kakakin rundunar Yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce, duk da iyayen matashin sun san cewar yana aikata laifukan Daba da shan miyagun kwayoyi, amma ba su taba sanarwar jami’an Yan sanda ba.

Ana zarginsa da hallaka wani mai suna Zaharaddin Iliyasu, ta hanyar yanka wuyansa da wukar Zarto sakamakon sumun sabani da suka yi da  marigayin.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ya ce jami’an yan sandan Panshekare ne suka samu nasarar cafke shi, a lokacin da yake kokarin guduwa jamhuriyar Nijar .

Yanzu haka dai ya na tsare a hannun yan sandan domin ci gaba da amsa tambayoyi kafin a gurfanar dashi a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *