Wata sabuwar ƙungiyar tawaye ta ɓulla a Jamhuriyar Nijar

Spread the love

Wata sabuwar ƙungiyar ‘yan tawaye, mai suna, Mouvement Patriotique du Niger, MPN, ta ɓulla a yankin arewacin Jamhuriyar Nijar.

Ƙungiyar tawayen ta Tubawa ta zama ta huɗu ke nan daga cikin jerin kungiyoyin tawaye masu faɗa da makamai da suka bayyana a ƙasar tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Waɗannan ƙungiyoyi na tawaye da suka bayyana daga yankin Agadez, da ke arewacin ƙasar na fafutuka ne don ganin an saki Mohamed Bazoum, wanda sojoji suka hamɓarar daga kan mulki, tare da mayar da ƙasar kan mulkin dumukuraɗiyya.

Wasu kungiyoyin ƙasar ta Nijar na ganin daukar makami ba mafita ba ce ga matsalolin siyasa kasar.

A watan Agusta na 2023, wani tsohon jagoran ‘yan tawaye kuma ɗan siyasa a ƙasar ta Nijar ya ce ya kafa wata ƙungiya a ƙoƙarin mayar da hamɓararren Shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki.

Rhissa Ag Boula ya ce ƙungiyar tasa mai suna Majalisar Nuna Bijirewa don Tabbatar da Jamhuriya (Conseil de la Résistance Pour la République) za ta tallafa wa ƙoƙarin mayar da gwamnati mai aiki da tsarin mulki a Nijar.

Yanzu dai bayanai na nuna cewa shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Abdourahmane Tchiani, a kwanakin nan yana ta ganawa da shugabannin ƙabilun yankin arewacin ƙasar da suka ɗauki makamai domin shawo kan matsalar, ta yadda za a sama wa ƙasar mafita – ta a gudu tare a tsira tare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *