Wata Ta Kotun Musulinci Ta Yanke Hukunci Kan Tuhume-tuhumen Da Ake Yi Wa Su Mata A Kano

Spread the love

Kotun shari’ar addinin Musulinci dake zaman ta a unguwar Danbare Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Mumzali Idris Gwadabe, ta yanke wa wasu Mata hukunci bayan ta same su da aikata Laifukan da ake tuhumar su.

Tun da fari Rundunar yan sandan jahar Kano, ce ta gurfanar da su bisa tuhumar su da hadin baki don aikata laifi, shiga waje ba da izini ba, cin mutunci da kuma bata Suna.

Wadanda ake tuhumar sun hada da Amina Umar, Zainab Abdullahi, Furera Umar da kuma Rukayya Umar , dukkansu dake Unguwar Hawan Dawaki.

Mai gabatar da Kara Bashir Wada, ya karanto mu su kunshin tuhume-tuhumen amma sun musanta su.

Sai dai kotun ta bukaci wadanda ake tuhumar su yi rantsuwa amma Suka ki amince wa, hakan ne ya kotun kotun ta yanke mu su hukuncin daurin watanni uku kowacce daga cikin su , ko biyan tarar naira dubu ashirin – ashirin tare da cike mu su takaddar zaman lafiya.

Idongari.ng ta ruwaito cewa, an same su da Laifin bata sunan Wata uwa da Yarta, da kuma ci mu su mutunci , inda Suka je har gidan su Suka ci zarafinsu sannan Suka ce yarta ta taba yin karuwanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *