Wata tawagar masu rajin kishin Najeriya ta gana da Shugaba Tinubu kan sauya kundin tsarin mulki

Spread the love

A Najeriya, wasu fitattun masu rajin kishin ƙasa daga sassa daban-daban, ƙarkashin jagorancin tsohon babban sakataren ƙungiyar ƙasashe renon Ingila (Commonwealth), Cif Emeka Anyaoku, sun shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da ya ɗauki matakin samar da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar.

Tawagar mutanen ta gabatar da buƙatar hakan ne, a lokacin da ta ziyarci Shugaban a Abuja, inda ta ba shi shawarwari da dama game da gaggan matsalolin da suka dabaibaye Najeriyar.

Ɗaya daga cikin ‘yan tawagar, Kwamared Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, ya sheda wa BBC cewa, sun bai wa Tinubun shawarwarin ne musamman batun kundin tsarin mulki saboda suna ganin yana daga cikin abubuwan da ke haifar wa da ƙasar matsala maimakon magance ta.

Sanatan ya ce, matsalolin sun danganci tsaro da siyasa da zamantakewa tsakanin al’ummomin ɓangarorin ƙasar daban-daban da kuma ɓarna da ya ce ana yi a gwamnati.

Ya ce tawagar tasu na ganin bai kamata a ce Najeriya tana da majalisun dokoki na tarayya biyu ba, wato ta dattawa da kuma ta wakilai, kamata ya yi a ce guda ɗaya ce, sannan ga ministoci wajen hamsin, kuma ga majalisun dokoki na jihohi duka ya ce wannan bai kamata ba, ganin irin ɗimbin kuɗaɗen da ake kashewa a kan haka.

Kwamared Sani ya ce, kamata ya yi a riƙa amfani da kuɗaden ƙasar wajen ayyukan cigaba da kuma taimaka wa talakawa.

Sannan ya ce akwai buƙatar samar da ma’aikatun tsaro na yankuna, domin hakan zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da ake fama da ita.

Tsohon sanatan ya ce, suna ganin muddin ba a samar da sabon kundin tsarin mulki ga najeriyar ba to haka za a yi ta tafiya a ƙasar.

Haka kuma ya ce tawagar tasu ta yi wa shugaban na Najeriya magana tare da ba shi shawara kan maganar zanga-zangar da ake yi a ƙasar, inda suka tuna masa cewa talakawa suna da ‘yanci a ƙarƙashin mulkin dumukuraɗiyya su yi zanga-zanga , ‘abin da ya kamata ya yi shi ne ya gayyato shugabannin da suka shirya ta ya tattauna da su a yi maslaha.”

”Sannan mun jawo hankalinsa a kan jami’an tsaro duk duniya akan yi zanga-zanga, jamian tsaro ya kamata su tsagaita amfani da makami wajen kwantar da mutane, akwai hanyoyi da yawa da za a kwantar da tarzoma ba tare da an dauki rayukan mutanne ba, ” in ji shi.

Ya ce shugaban na Najeriya ya yi alƙawarin duba shawarwarin da suka ba shi, tare da gayyatar jagoran tafiyar Chief Emeka Anyaoku nan gaba kadan kan batutuwan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *