Kotun majistiri mai 47 dake NormanSland Kano, karskashin jagorancin mai shari’a, Hadiza Muhd Hassan, ta yanke wasu yan Tiktok hukuncin daurin shekara daya a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya, saboda da samun sa da aikata laifin yada Fitsara a dandanlin Tiktok.
Hukumar ta ce fina-finai ta jihar ce, ta cafke mutanen biyu, da suka hada da Ahmad Isah da kuma Maryam Musa, dukkan mazauna uguwar Hotoro, inda hukumar ta mikawa jami’an yan sanda su kuma suka gurfanar da su a gaban kotun.
Mai gabatar da kara kuma lauyan gwamnatin Kano, Barista Garzali Maigari Bici, ya bukaci kotun ta bayar da damar karanto mu su kunshin tuhume-tuhumen da ake yi mu su, kuma kotun ta amince.
- Yan Sandan Kano Sun Gurfanar Da Wasu Mata Da Ake Zargi Da Yin Barin Zance Ga Wata Mata
- Cikin Hotuna: Yansanda Sun Kwato Motoci 7 Da Aka Sace Da Taimakon Na’urar e-CMR A Kano
An karanto mu su kunshin tuhumar, hada baki wajen aikata laifi da yada kalaman fitsara a kafar Tiktok, kuma dukkansu sun amsa laifinsu da ake tuhumarsu.
Sai dai Maryam Musa, ta fashe da kuka a cikin kotun .
Kotun ta yankewa mu su hukuncin daurin shekara daya ko zabin biyan tarar naira dubu 100,000. Kowannensu.
Sannan kotun ta hore su , su zama mutanen kirki tare da cewar za su rubuta takaddar zaman lafiya.
Tunda fari ana zarginsu da yada wani Faifen bidiyo mai suna (Ana yi Short) mai dauke da kalaman fitsara wanda ake zargin zai Sanya damuwa a zukatan jama’a.