Watan Ramadan: Hukumar Tace Fina-finai Ta Bada Umarnin Garkame Gidajen Gala A Jahar Kano

Spread the love

Hukumar tace Fina-finai da Dab’i ta jahar Kano ta bada umarnin kulle dukkannin gidajen Galar dake fadin jahar Kano.

Wannan na zuwa ne biyo bayan wata gana wa da Shugaban Hukumar ya yi da jagororin yan Kungiyar ta ma su gidajen galar reshen jahar Kano a ofishin sa.

A cewar shugaban hukumar Abba El-Mustapha, dokar zata fara aiki ne tun daga yau lahadi har zuwa 1 ga watan shawwal wato ranar bikin karamar sallah.

Ranar Mata: Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Kotun Cin Zarafin Jinsi

gSojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga uku a dajin Sambisa

Abba El-mustapha ya gargadi ma su gidajen wasannin na gala da su guji Karya doka domin duk wanda Hukumar ta samu da laifin karya wannan dokar to hakika zata dauki tsattsauran mataki a kansa, wanda ka iya sawa ya rasa lasisin sa na din-din-din

Elmustapha ya kuma godewa jagorori tare da yan Kungiyar ta ma su gidajen gala hadi da al’ummar jahar Kano dangane da hadin kan da suke ba wa Hukumar a kowanne lokaci.

A karshe ya Kara tunatar da dukkannin al’umma cewa kofar sa abude ta ke domin ba shi shawara ko sanar da Hukumar duk wani al’amari da zai taimake ta don samun nasarar aiyukan da ta sanya a gaba .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *