Wike ya kira taron gaggawa kan taɓarɓarewar tsaro a Abuja

Spread the love

Ministan babban birnin Najeriya Nyesom Wike ya kira taron gaggawa kan taɓarɓarewar tsaro a Abuja.

Ƴan bindiga a baya-bayan nan suna kai farmaki kan gidaje tare da sace mutane.

Lamarin da ke ɗaga hankalin al’umma, ya kai maƙura ne bayan da aka samu labarin kisan Nabeeha – ɗaya daga cikin ƴan mata shida ‘yan gida daya da ƴan bindiga suka sace a farkon watan nan na Janairu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Wike, a jawabin da ya yi a taron, yana yi wa mazauna birnin Najeriyar albishir da cewa za a tabbatar da tsaro a birnin.

Ya ce gwamnati tana aiki da hukumomin tsaro domin dakile matsalar rashin tsaron.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugabannin hukumomin tsaro a Abuja da kuma sarakunan gargajiya.

Wike ya jaddada buƙatar hukumomin tsaro su sake lale su kuma ƙara ƙaimi domin shawo kan matsalar tsaron a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *