‘Ƴan Najeriya za su wahala idan NLC ta ci gaba da yajin aiki’

Spread the love

Ministar ƙwadago ta Najeriya, Nkeiruka Onyejeocha, ta ce ƴan ƙasar su sha wuya idan har ƙungiyar ƙwadago ta NLC, ta kafe kan ci gaba da yajin aikin da suka kira.

Nkeiruka Onyejeocha, ta bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da ita a tashar talabijin ta Channels, bayan da shugabannin ƙwadagon suka jagoranci yajin aiki na sai abin-da-hali-ya-yi daga jiya Litinin, a kan maganar mafi ƙanƙantar albashi a Najeriya.

Ministar ta ce tana fatan za a samu matsaya a kan batun albashin, amma tafiya yajin aiki abu ne da ke tattare da illoli ga tattalin arziƙin ƙasa da kuma rayuwar jama’a.

Onyejeocha ta ce, ”idan yajin aikin ya ci gaba, ƴan ƙasa za su wahala, kuma tuni ma har sun fara wahala. Ɗalibanmu da ya kamata su rubuta jarrabawa lamarin ya shafe su saboda sun rasa ababen hawa da za su je wuraren jarrabawar.”

Ta ƙara da cewa, ”akwai kuma mutanen da ba su da abin da za su ci sai sun je wuraren aikinsu sun nema. Wasu mutanen da ke aiki a sakatariya kullum sun dogara ne a kan abin da suke samu a ofisoshin.

”Sannan a ɓangaren yin ayyuka da abubuwa, mun san cewa idan aka dakatar da ayyuka, hakan zai shafe tattalin arziƙinmu,” in ji ministar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *