Dakarun da suka kewaye wurin tattaunawa da NLC masu gadin Ribadu ne – Sojin Najeriya

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin da ƙungiyar ƙwadago ta yi cewa sojoji sun kewaye wurin da suke tattaunawa da wakilan gwamnatin ƙasar, tana mai cewa masu kare mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro ne.

Ɗazun nan muka kawo muku rahoton cewa NLC ta yi zargin sojoji sun yi wa ofishin sakataren gwamnatin tarayya tsinke yayin da suke ganawa da wakilan gwamnati kan yajin aikin da suke yi.

Sai dai cikin wani martani da ta mayar a kan saƙon da NLC ta wallafa a dandalin X, rundunar sojan ta ce mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu suke bai wa kariya.

“Ku sani cewa Mallam Nuhu Ribadu ma na halartar ganawar kuma ya isa wurin ne da sojoji masu gadinsa da doka tanada,” in ji saƙon.

“Da zarar ganawar ta ƙare jami’an tsaron za su fice tare da shi daga wurin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *