Gwamnatin Najeriya ta ce yajin aikin da ƴan kwadago ke yi ya saɓa wa doka

Spread the love

Ministan shari’a na Najeriya Lateef Fagbemi ya ce yajin aikin da manyan ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar suka fara a yau kan mafi ƙanƙantar albashi ya saɓa wa doka.

Babban lauyan na gwamnati ya bayyana hakan ne bisa dalilin cewa ƙungiyoyin ba su bi ka’idojin da dokar ƙwadago ta gindaya ba, kamar yadda tashar talabijin ta Channels ta ruwaito.

Maganar ta biyo bayan manyan ƙungiyoyin ma’aikata biyu na ƙasar, NLC da TUC, ne da suka fara yajin aikin sai baba-ta-gani daga yau Litinin bayan gwamnati ta gaza cika wa’adin ranar 31 ga watan Mayu na aiwatar da ƙarin albashi mafi ƙanƙanta da kuma rage farashin wutar lantarki.

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta NLC da TUC sun ce za a fara yajin aikin har sai sun sami sabon albashi mafi ƙanƙanta na ƙasa kuma har sai gwamnati ta yi da gaske.

Ƙungiyoyin ƙwadagon na son a sanya albashi mafi ƙanƙanta kan dala $334, kwatankwacin N494,000 kenan inda kuma gwamnati ta tsaya a kan Naira 30,000, kwatankwacin dala 22, duk wata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *