Kotu ta tura shugabannin zanga-zangar Katsina gidan yari wata ɗaya

Spread the love

Wata kotu a jihar Katsina ta tura 7 daga cikin jagororin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a ƙasar, gidan yari tsawon wata ɗaya.

Wani makusancin biyu daga cikin jagororin ya shaida wa BBC cewa, a ranar Juma’a 9 ga watan Agusta 2024, rundunar ‘yansanda ta jihar ta gurfanar da Kwamared Habibu Ruma da Kwamared Kabir Shehu ‘Yanɗaki da kuma wasu mutum biyar a gaban kotun majistare a birnin Katsina, inda ta tuhume su da laifukan da suka haɗa da tarzoma da sata da kuma ɓarnata kayan gwamnati.

Bayan an karanta musu laifukan da ake tuhumarsu da su, ”sai kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar 11 ga wata mai zuwa, Satumba, 2024 tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare mutanen bakwai a gidan kaso, zaman waƙafi.

A Najeriya an gudanar da zanga-zanga ta gama-gari daga ranar 1 ga watan Agusta, 2024 zuwa 10 ga watan na Agusta 2024, saboda matsaloli da suke addabar ƙasar, waɗanda suka haɗa da tsadar rayuwa da rashin tsaro musammana a arewacin da neman shugabanci na gari.

Sai dai yayin da zanga-zangar ta kasance cikin lumana a wasu jihohin, a wasu kuwa ta rikiɗe ta zama tarzoma inda aka riƙa sace-sace da ɓarnata kayan gwamnati da na ‘yan kasuwa da ɗaiɗaikum mutane.

Tarzomar ta kuma yi sanadin kashe mutane da jikkata wasu da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *