Majalisar Dattijan Najeriya ta soki jihohi kan rashin kyakkyawan shirin aikin hajji

Spread the love

Majalisar dattijan Najeriya ta soki lamirin wasu jihohin ƙasar kan yadda suka gaza yin shiri mai kyawu a aikin hajjin da ke gudana yanzu haka a ƙasar Saudiyya.

Ko a shekarun da suka gabata mahajjata sun sha kokawa kan matsalar masauki da na abinci, lamarin da ya rataya a wuyan hukumomin kula da mahajjata na jihohi.

A tattaunawarsa da BBC, shugaban kwamitin kula da aikin hajji na Majalisar Dattijan Najeriya, Ali Ndume, ya ce sun damu matuƙa game da rashin kyakkywan makwancin mahajjata a filin Mina, inda aka samu cunkoso mai yawa.

Ya ce: “Babbar matsalar da aka samu ta faru ne a filayen Mina da Arafat da kuma wajen jifa”.

Ya ƙara da cewa “lamarin ya jefa mutane cikin mawuyacin hali, sansanin da aka ba su akwai matsi, ya yi cunkoso ƙwarai da gaske”.

“Katifar da aka bai wa mahajjata ƙarama ce sosai kuma an harhaɗa su a matse…Inda wata cuta ta ɓarke da za a iya samun matsaloli sosai”.

Wannan na zuwa ne yayin da mahajjata a ƙasar ta Saudiyya suka koka kan zafin yanayi.

Lamarin da ya yi sanadiyyar mace-macen maniyyata da dama.

Ƙasar Jordan ta bayyana cewa alhazanta guda 14 ne tsananin zafi ya yi sanadiyyar rasuwarsu a ƙasar ta Saudiyya sa’ilin aikin hajjin na wannan shekara.

A ɓangare guda, sanata Ali Ndume ya nuna damuwa kan yadda aka ajiye mahajjata a wuri mai nisa a Mina da kuma wajen jifan sheɗan.

Ya ƙara da cewa hakan na nuna cewa an samu tangarɗa wajen shirye-shiryen aikin hajjin bana.

Ya kuma alaƙanta waɗannan matsaloli ga jihohi, musamman na arewacin Najeriya waɗanda ke da mahajjata masu yawa, waɗanda ya ce ba su yi shirin da ya kamata ba.

Sanata Ndume ya ce bayan kammala aikin hajjinna bana, kwamitinsa zai tattauna da hukumar alhazai ta Najeriya da kuma na jihohi domin ganin an hana faruwar irin haka a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *