Muna so a binciki El-Rufai kan korar ma’aikata 27,000 da ya yi – PDP

Spread the love

Jam’iyyar hamayya ta PDP jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya ta bai wa kwamitin da Majalisar jihar ta kafa domin binciken kashe-kashen kudaden da gwamnatin El-Rufai ta yi, da ya binciki tsohon gwamnan kan korar ma’aikata 27,000 da ya yi a faɗin ƙasar ba tare da biyansu haƙƙoƙinsu ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa cikin wata sanarwa da Sakataren hulɗa da jama’a na Jam’iyyar Alberah Catoh ya fitar, ta ce, PDP ta yi watsi da abin da ta kira ‘lalata aikin gwamnati’ a jihar Kaduna.

Catoh ya bayyana haka a yayin bikin Ranar Ma’aikata ta 2024, inda ya ce jam’iyyar a ko da yaushe na nuna goyon bayanta ga ma’ikata kan juriya da yadda suke gudanar da ayyukansu a Najeriya baki daya.

“Muna kira ga kwamitin da Majalisar Jihar Kaduna ta kafa da zai yi bincike kan El-Rufa’i da ya sake fadada bincikensa har zuwa kan korar ma’aikata 27,000 da aka yi bisa rashin adalci a fadin jihar ba tare da an biya su hakkokinsu ba, kuma wannan ‘nuna halin ko in kula ne ga aikin gwamnati,” kamar yadda yake cikin sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *