Najeriya za ta rage lantarkin da take bai wa Nijar da Benin da Togo

Spread the love

Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) ta umarci kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasar ya rage lantarkin da yake bai wa ƙasashe maƙwafta domin bunƙasa samar da wutar lantarki a cikin gida.

A cikin wata takardar umarni da hukumar ta fitar a ranar Juma’ar da ta gabata, ta ce tsarin da kamfanin samar da wutar lantarki ga ƙasashen ƙetare ke bi a halin yanzu ya jawo jefa ‘yan Najeriya cikin wahala.

Hukumar ta ƙayyade cewa kashi 6 cikin 100 na wutar da ake samarwa ne kawai za a fitar da su ƙasashen ƙetare na tsawon watanni shida masu zuwa, daga ranar 1 ga Mayu.

Akwai yarjeniyoyi da Najeriya ta ƙulla na samar da wutar lantarki ga ƙasashen Afirka da ke makwabtaka ita.

Ana yawan samun katsewar wutar lantarki a Najeriya saboda karancin wutar amma abin ya ƙara kamari a ‘yan kwanakin nan.

A baya-bayan nan ne kamfanonin samar da wutar lantarki suka ƙara kuɗin lantarki ga wasu kwastomomin cikin gida da ke samun wutar lantarki na tsawon sa’o’i 20 a kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *