NDLEA ta kama ƙwayoyin da aka yi yunƙurin safararsu zuwa Amurka ta Birtaniya

Spread the love

Jami’an Hukumar Yaƙi da sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) sun kama wasu nau’o’in hodar ibilis da ƙwayoyi da suka haɗa da tramadol da allurar pentazocine da kuma morphine sulfate, da aka ɓoye a cikin talkalma da tufafi da za a yi jigilar su zuwa Amurka da Ingila, da kuma Cyprus.

Cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin kakakin hukumar, Femi Babafemi, ta bayyana nasarorin da ta samu a yaƙin da take yi fataucin miyagun ƙwayoyi a sassa daban-daban na ƙasar.

Sanarwar ta ce jami’an hukumar sun kama kimanin gram 250 na hodar iblis da aka ɓoye a cikin takalman da za a kai CYprus, sa’annan an samu sama kilogiram biyar na ƙwayoyi da ke kan hanyar zuwa Amurka da Birtaniya cikin kayayyakin gida da aka yi nufin safarrasu ta hanyar amfani da wasu kamfanonin jigilar kayayyaki da ke Legas.

Haka kuma jami’an hukumar sun kama wani nau’in tabar wiwi da ake kira Loud mai nauyin gram 440 da aka shigo da ita daga kasar Kanada zuwa Legas.

A wani samame da hukumar ta kai a dajin Ohen da ke yankin Abudu a jihar Edo a ranar Alhamis din ta gabata, jami’anta sun lalata tabar wiwi mai nauyin kilogiram sama da dubu biyar a wani gona mai fadin hekta 3,000, inda aka kama mutum huɗu.

Hakazalika, hukumar ta kama sama da kilogiram 2,000 na kayayyakin da ake haɗa kayan maye na Akurkura, a wani rumbun ajiya a garin Konduga na jihar Borno a ranar Talata 9 ga watan Yuli yayin da jami’an NDLEA suka gudanar da wani aikin haɗin gwiwa tare da dakarun sojoji da ke yankin

Sanarwar ta ƙara da cewa a ranar laraba da ta gabata jami’an hukumar sun kama wani mutum mai shekaru 54 da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 47 a cikin garin Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *