Tsohon darakta kuɗi na Babban Bankin Najeriya, CBN, Ahmed Bello Umar, ya ce sabon kuɗin da aka sauya wa fasali da tsohon gwamnan Bankin, Godwin Emefiele ya gabatar a ƙarshen shekarar 2022, ba shi ne ainihin sabon fasalin da tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya amince masa ba.
Yayin da yake bayar da shaida a gaban kotu ranar Talata kan shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan Bankin, tsohon daraktan kuɗin ya ce mista Emefiele bai yi amfani da fasalin da shugaan ƙasar ya amince da shi ba.
Ya faɗa wa kotun cewa akwai bambanci mai yawan gaske tsakanin fasalin takardun kuɗin da tsohon shugaban ya sahale da kuma wanda Emefiele ya buga.
A ƙarshen shekarar 2022 ne dai tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari, ya amince da sauya fasalin kuɗin ƙasar, wani abu da ya janyo ce-ce-ku-ce mai tarin yawa a ƙasar.
Sakamakon yadda gwamnati ta sanya wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kuɗin, wani abu da ya jefa al’ummar ƙasar cikin fargabar tafka asara.
To sai dai bayan shigar da ƙara da wasu gwamnonin ƙasar suka yi, Kotun ƙolin ƙasar ta tsawaita wa’adin da shekara guda, inda daga baya kuma ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da kuɗin har zuwa abin da hali ya yi.