Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta yi iƙirarin cewa dakarun soja sun kewaye ginin da suke tattaunawa da wakilan gwmanatin tarayya a yammacin yau.
Ana gudanar da tattaunawar ne a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume da ke Abuja.
“Yanzu haka sojoji ne ke kewaye da wurin da ake ganawa tsakanin ‘yan ƙwadago da gwamnati a ofishin sakataren gwamnatin tarayya,” kamar yadda NLC ta wallafa a shafinta na X.
“Za mu yaƙi duk wani yunƙurin tilastawa, ko tsokana, ko ɓata sunan shugabanninmu a wurin tattaunawar kuma mu tsawaita yajin aikin.”
Ana sa ran wannan tattaunawar share fage ce kafin wadda za su sake yi a gobe Talata.