Wuya ta sanya ECOWAS Ta Ɗage Takunkumin Da Ta Sanya Wa Nijar Albarkacin Watan Azumin Ramadana

Spread the love

Ƙungiyar Bunkasa Tattalin Arziki Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS, ta ɗage takunkumin da kakabawa Jamhuriyyar Nijar a sanadiyyar juyin mulki da sojoji suka yi watanni bakwai da suka gabata.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Nijeriya, Abdulaziz Abdulaziz ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A cewar saƙon da ya fitar a Yammacin wannan Asabar ɗin, hadimin Shugaban Kasar ya ce an ɗage takunkumin ne domin tausaya wa talakawa albarkacin watan Azumin Ramadana da ya ƙarato.

Abdulaziz ya ce, “Domin tausaya wa al’umma musamman a wannan lokaci da azumi ke gabatowa, shugabannin ECOWAS sun amince da ɗage takunkumin rufe iyaka da yanke wuta da aka dorawa ƙasar Nijar tun bayan juyin mulki.”

ECOWAS dai ta cimma wannan matsaya ce a ranar Asabar a yayin taron da ta gudanar a Abuja, inda kuma ƙungiyar ta sanar da janye takunkumin da ta saka wa kasar Guinea.

Tun a farkon watan nan ne Mali da Burkina Faso da Nijar suka sanar da ƙungiyar kan niyyarsu ta barin ƙungiyar, wanda wannan sabon lamari ne tun bayan kafa ƙungiyar a 1975.

Yadda masu kuɗi ke lalata ƴaƴan talakawa a Kano – Daurawa

EFCC ta kama mutum 27 kan zargin zamba ta intanet a Bauchi

Sai dai tun a jawabinsa na farkon Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, “dole ne mu sake nazari kan hanyar da muka ɗauka ta neman tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasashe mambobinsu.

“Saboda haka ina kira a gare su da su sake nazari dangane da matakinsu na ficewa daga gidansu haka kuma kada su ɗauki ƙungiyarmu a matsayin abokiyar gaba,” kamar yadda Tinubu ya ƙara da cewa.

Tun a makon da ya gabata ne Shugabannin ECOWAS sauka ɗaura haramar gudanar da taro a ƙarshen wannan makon don nazari kan takunkuman da aka kakaba wa kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar.

AMINIYA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *