Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi ll, ya ce ya kamata gwamnati ta riƙa cizawa tana hurawa game da haraje-harajen da take ƙaƙaba wa al’umma.
Muhammadu Sanusi ll ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron kan tattalin arziki da zuba jari na 2024 da aka gudanar a birnin Fatakwal na jihar Rivers.
Ya kafa hujja da maganar tsohuwar firaministan Birtaniya, Margaret Thatcher, wadda take cewa babu ƙasar da da za ta samar da ci gaba ta hanyar tatsar al’ummarta.
Ya ce duk da cewa karɓar haraji na da muhimmanci, amma bai kamata a tsawwala wa jama’a ba, ”ya kamata gwamnati ta karɓi haraji domin ci gaban ƙasa, ba domin samun riba ba”.
- Majalisar dokokin Kano ta miƙa wa gwamna sabuwar dokar masarautu
- An kuɓutar da ‘ya’yan ɗan majalisar Zamfara bayan wata 17 da sace su