Ya kamata a rusa hukumar Nahcon saboda ta gaza – Bago

Spread the love

Gwamnan jihar Neja Mohammed Umar Bago ya bayyana rashin gamsuwarsa kan yadda hukumar alhazan Najeriya Nahcon ta gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji bana.

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Saudiyya game da yadda aka gudanar da aikin, Gwamna Bago ya yi kira ga majalisar dokokin ƙasar ta binciki Nahcon kan yadda ta kashe kuɗin tallafin aikin hajji na naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bai wa hukumar.

Gwamna Bago ya ce a matsayinsa na gwamna zai buƙaci ƙungiyar gwamnonin ƙasar ta yi kiran rusa hukumar Nahcon, saboda a cewarsa hukumar ba ta da wani amfani, ta gaza ta kowane fanni.

Ya ce ya kamata shirya aikin Hajji ya koma ƙarƙashin ikon jihohi ba gwamnatin tarayya ba.

”Gwamnatin tarayya ta girmi shirya aikin Hajji, wannan abu ne da ƙaramar hukuma za ta iya shiryawa, don haka ina kira a bar jihohi su riƙa shirya aikin Hajjin jihohinsu, kamar yadda wasu ƙasashen duniya ke yi”.

Gwamnan ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ya ce Nahcon ta kasa samar wa gwamnoni da sauran manyan mutane masaukai a Minna.

”A ce kakakin majalisar wakilai na Najeriya da wasu gwamnoni sun kasa samun wurin da za su kwanta a filin Minna wannan abin takaici ne”.

”Wasu na cewa muna ƙorafin ne saboda abin ya shafe mu, haƙiƙa ya shafe mu saboda haka lokaci ya yi da za mu tashi mu yi kiran a mayar da shirya aikin Hajji ƙarƙashin jihohi”, in ji gwamnan.

Gwamnan ya kuma koka kan yadda ya ce mahajjata sun biya kuɗi masu yawa amma suka kasa samun wadataccen kuɗin guzuri daga Nahcon.

”Ta yaya mutum zai biya naira miliyan takwas amma ace dala 400 kawai za a ba shi? wannan abu ne da hankali ba zai ɗauka ba”.

Gwamna Bago ya kuma koka kan abinci da masaukai da hukumar Nahcon ta tanadar wa mahajjatan ƙasar.

Ya ƙara da cewa kamata ya yi hukumar Nahcon ta zama mai lura da ayyukan Hajji ba mai gudanar da shirye-shiryen aikin hajji ba.

Ya ce alhazan jihar Neja biyu ne suka rasu sakamakon rashin lafiya, yayin da huɗu suka mutu saboda tsananin zafi

Sai dai gwamnan ya ɗora alhakin mutuwar mutanen biyu – da suka rasu sakamakon rashin lafiya – kan hukumar Nahcon.

Ya ce inda hukumomin alhazan jihohi ne ke lura da lafiyar alhazan jihohin da an samu sauƙi wajen saurin gano cutar da alhazan ke ɗauke da ita da kuma magance ta makar yadda ya kamata.

”Amma babu wanda ya yi hakan, saboda Nahcon ce ke lura da ɓangaren lafiyar alhazai”

Gwamnan ya ce kamata ya yi hukumomin alhazai na jihohi su lura da alhazan jihohinsu.

”Ya kamata a bar jihohi su riƙa tantance alhazansu, su san irin lalurorin da alhazan ke ɗake da su, tare da irin magungunan da suke sha, domin sanin matakan da za su ɗauka na lura da waɗanna alhazan, amma babu wanda ya yi hakan , saboda Nahcon ce ke da alhakin gudanar da hakan” in ji shi.

Ba wannan ne karon farko da wani gwamna a Najeriya ya yi ƙorafi kan yadda hukumar Nahcon ta tafiyar da ayyukan Hajjin bana ba.

Ko a makon da ya gabata ma jaridun ƙasar sun ambato gwamnan jihar, Bauchi Sanata Bala Mohammed na ƙorafin yadda hukumar Nahcon ta tafiyar da shirye-shiryen aikin Hajjin na bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *