Ministan Shari’a na Najeriya, Lateef Fagbemi ya ce akwai buƙatar rushe hukumomin zaɓe na jihohi waɗanda ya bayyana da babban dalilin da lalacewar al’amura ga ci gaban ƙananan hukumomi.
Ministan ya faɗi hakan ne yayin wata tattaunawa kan wani maudu’i na Matsalolin tsaro a Najeriya da shugabanci a matakin ƙananan hukumomi ranar Litinin a Abuja.
Ministan ya ƙara da cewa gwamnoni sun fake kan gazawar sassan tsarin mulkin Najeriya na 1999 wajen kassara ƙananan hukumomi.
Mista Fagbemi ya ce babban abin da gwamnoni ke amfani da shi wajen daƙile cigaban ƙananan hukumomin shi ne amfani da hukumomin zaɓe na jihohi ta hanyar ɗamfara wa jama’a shugabannin da suke so.
Minsitan daga ƙarshe ya kuma nuna irin illar amfani da asusun bai ɗaya ga jihohi da ƙananan hukumomi wani abu da ya ce shi ma yana cikin abubuwan da suka illata ƙananan hukumomi ta hanyar riƙe kuɗaɗen da suka kamata su je ga ƙananan hukumomin.
- Ana Zargin Wani Matashi Da Kashe Mahaifiyarsa A Kano
- Sai yau Litinin muka karɓi umarnin kotu kan sauke Aminu Ado – Gwamnatin Kano