Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obansanjo ya shawarci al’ummar Afirka su sake nazarin tsarin dimokraɗiyyar da Turawan Yamma suka gasar musu.
Gidan talbijin na Channel a Najeriya, ya ambato mista Obasanjo na cewa dole ne ƙasashen Afirka su gina tsarin dimokraɗiyyar da zai dace da al’adu da ɗabi’un al’ummar yankin.
Mista Obasanjo ya bayyana hakan ne a wani taro kan dimokradiyyar nahiyar Afirka da aka gudanar a ɗakin taro na Yar’adua Centre da ke Abuja babban birnin ƙasar.
- Jami’an tsaro sun yi wa majalisar dokokin Cross River tsinke bayan tsige kakakinta
- Jami’an tsaro sun yi wa majalisar dokokin Cross River tsinke bayan tsige kakakinta
Tsohon shugaban ƙasar ya ce lokaci ya yi da al’ummar Afirka za su ajiye tsarin da turawa suka gadar musu, su gina nasu wanda zai dace da ala’dunsu.
Ya kuma ce yana da kyau shugabannin Afirka su nuna kishi da kan ci gaban al’umominsu.
Obasanjo ya ce idan ana son dimokraɗiyya ya yi aiki a Najeriya da ma Afirka baki-ɗaya, dole ne a gina shi kan tsarin shugabanci na gari, ta hanyar bai wa doka ta yi aiki.
Tsohon shugaban ƙasar, ya sha sukar yadda ake gudanar da tsarin dimokraɗiyya a Najeriya da ma ƙasashen Afirka.
- Majalisar dokokin Katsina ta gargaɗi MTN kan yawan katsewar sabis
- Soja Ya Sumar Da Wata Da Mari A Abuja