Shugaban kasuwar Galadima da ke birnin Kano, Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya bayyana damuwar sa akan yadda masu sayar da man girki a tsakanin al’umma, musamman a unguwanni ba sa rage farashin man, ko da kuwa an ɗan sami sauƙi daga inda suke sarowa.
Da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa, Shugaban Kasuwar ta Galadima ya bayyana cewa kowa ya sani a watannin baya an sami hauhawar tsadar man girki, amma cikin ikon Allah yanzu Allah ya juya lamarin ana samun sauƙi da ya fi a ce ƙaruwa yake a harkar mai an sami ragi.
Ya ce, amma yana mamakin wani ya ce man bai rage kuɗi ba, ya rage kuɗi tunda jarkar man da ya kai ₦95,000 a baya, yanzu ba ya wuce ₦82,000 zuwa 83,000 aƙalla an sami saukin ₦15,000 ko da ₦10,000, ka ga an samu sauƙi akan yadda yake a da.
- NDLEA Ta Kama Wata Mata Da Yayanta 2 Da Zargin Safara Da Siyar Da Kayan Maye A Kano
- Yan Sanda Sun Cafke Matashiyar Da Ake Zargi Da Jagorantar Satar Wayoyin Mata A Kano
Ya ce, illa iyaka dai yana jin labarin cewa wai a cikin gari mutane da suke sayar wa jama’a ba su rage ba, amma a gaskiya su a kasuwa sun rage an sami sauƙi, ba a ci gaba da samun hauhawar yanzu sauka ma ake samu na kayan.
Daga nan sai Alhaji Mustapha Shu’aibu ya yi kira ga dukkan jama’a masu sayar da mai a cikin gari, yadda su ma suka sami sauƙi, to su rage wa jama’a, Allah ya kawo rahama ba, ta su ba ce su kaɗai ta kowa da kowa ce.