Ya Kamata Najeriya Ta Gina Katanga A Kan Iyakokinta – CG Musa

Spread the love

Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa ya nuna buƙatar gina katanga a ilahirin iyakokin ƙasar da maƙwaftanta domin kare kwararar masu ɗauke da makami zuwa cikinta.

Yanzu haka dakarun sojin Najeriya na fafutikar ganin sun yaƙi matsalar tsaro da ke addabar ƙasar, musamman rikicin Boko Haram da ƙasar ta kwashe shekara 16 tana fama da shi a arewa maso gabas.

Mayaƙan ƙungiyar – wadda ta samo asali daga kungiyar IS reshen yammacin Afirka – sun kashe jami’an tsaro da dubban fararen hula, yayin da rikicin ya tagayyara miliyoyi.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato Janar Christopher Musa a wani taron tsaro da ke gudana a Abuja yau Talata a Abuja na cewa “kula da kan iyakoki abu ne mai muhimmanci,” inda ya bayar da misali da iyakar ƙasar Pakistan mai katangar da ke da tsawon kilomita 1,350 tsakaninta da Afghanistan, da kuma Saudiyya wadda ke da katanga mai tsawon kilomita 1,400 tsakaninta da Iraqi, a matsayin kyawawan misalai.

Wannan ne karon farko da wani babban jami’in gwamnatin Najeriya ke bayar da irin wannan shawara a bainar jama’a.

“Wasu ƙasashen sun yi katanga a kan iyakokinsu sanadiyyar matsalar tsaro,” in ji Janar Musa.

Najeriya ta yi iyaka da ƙasashen Nijar da Kamaru da Benin da kuma Chadi, waɗanda dukkaninsu ke fama da rikicin ƴanbindiga.

Hukumomin Najeriya sun sha ɗora laifin matsalar tsaron da ƙasar ke fama da ita a akan kutsen mayaƙa daga ƙasashen ƙetare.

Iyaka mafi tsawo da Najeriya ke da ita da wata ƙasa ita ce tsakaninta da Kamaru ta ɓangaren gabas – mai nisan kilomita 1,975 – yankin da rikicin Boko Haram ya yi katutu.

Sai kuma iyaka mai tsawon kilomita 1,500 da Jamhuriyar Nijar, da kuma iyaka mai tsawon kilomita 80 da ƙasar Chadi, waɗanda dukkaninsu ke fama da matsalar kwararar masu ɗauke da makamai.

Janar Musa ya yi gargaɗin cewa kallon tarin arziki da ake yi wa Najeriya ya sanya kowa ke aniyar kaiwa cikinta. “Kowa Najeriya kawai yake hari. Wannan ne dalilin da ya sa muke buƙatar kare iyakokinmu,” in ji shi.

“Wannan na da matuƙar muhimmanci ga wanzuwarmu da kuma ƴancinmu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *