Ya Maka Surukinsa A Kotu Kan Kudin Tsintuwa

Spread the love

Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu Kano, ta ci gaba da sauraren karar da wani magidanci da ke zargin matarsa da mahaifinta da cin amana da kuma boye wasu kudi da dansa ya tsinta kimanin shekaru biyu da suka gabata.

Lauyan mai kara Abdurrrahman Sulaiman ya shaida wa kotun cewa yaron ya tsinti wasu bandira 50 na kudin Dalar Amurka a Tudun Fulani da ke unguwar Darmanawa a yankin Karamar Hukumar Tarauni.

Amma sai matarsa, mahaifyar dan, ta dauki kudin ta ba wa mahaifinta cewa zai ajiye tsawon shekara guda.

Amma daga baya sai ya ci amana ya hau kan kudin ya zauna ya kuma hana mai kara kasonsa.

A cewar lauyan mai karan, “lokacin da shi mai kara ya fuskanci surukin nasa yana amfani da wadannan kudade ta hanyar yin bushasha a gidansa inda ya yi wa ’ya’yansa uku aure, ya kuma bude manyan shaguna a Kasuwar Kantin Kwari da sauransu.

“Don haka sai ya nemi a ba shi wani abu daga kudin kamar yadda aka yi alkawari a baya cewa za a ba shi wani babban kaso daga kudin tare da gina masa gida da kuma kara masa jari da sauransu.

Amma sai surukin nasa ya shafa wa idanunsa toka ya nuna bai san maganar kudi ba kwata-kwata.”

Shi ma a nasa jawabin lauyan wadanda ake kara Barista Bashir Muhd Muqaddam, ya musanta batun tsintar kudin, inda ya ce iya sanin su yaron Haneef ya tsinci wata tsohuwar karamar jaka inda mahaifiyarsa ta karba ta ajiye a daki.

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

Kotu ta aike da yar Tiktok Ramlat Princess gidan gyaran hali bisa zargin yada badala

Lokacin da yaro ya ba mahaifinsa labarin tsintuwar da ya yi sai ya sami matarsa ya tambaye ta ina kudin da ya tsinta, inda ita kuma cikin mamaki da wasa ta ce masa ta kai wa mahaifinta.

“Tun daga wannan lokaci ba a sake yin maganar ba har zuwa lokacin da aka fara juya maganar a dangi; Ana zargin ta da mahaifinta.

Duk da ta tabbatar da cewa ba ta san maganar kudi ba sai jakar walet, amma ba a yarda da ita ba, har sai da lamarin ya kai da ta bar gidan mijinta nata na wani lokaci kafin daga bisani a yi musu sulhu a Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.”

A cewar lauyan, “mahaifin matar bai ma san maganar tsintuwar kudi ba, sai bayan shekara guda da aka fara juya maganar a dangi ana zargin sa da shi da ’yarsa.

“Kuma ya tabbatar da cewa babu wasu kudi da ’yarsa ta ba shi ajiya haka kuma bai yi wani alkawari da kowa a kan batun kudin ba.”

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya bayar da umarnin da a kawo yaron gaban kotun domin yi masa wasu tambayoyi.

Daga nan kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Janairu 2024 domin ci gaba da shari’ar.

AMINIYA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *