Al’ummar unguwar Kundila dake karamar hukumar Tarauni Kano, sun wayi garin yau litinin da tsintar gawar wani matashi mai suna Atiku Sulaiman, wanda ake zargin ya rasa ransa lokacin da yake kokarin satar wayar wutar lantarki.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa sunga matashin kwance da wani zarto a hannunsa kuma wasu sassan jikinsa ya sabule sanadiyar jan da wutar lantarki ta yi masa.
Lamarin dai ya faru ne lokacin da matashin yake yankar wayar da wani zarto, inda aka kawo wutar lantarki wanda hakan ya janyo rasa ransa.
Shaidu gani da idon sun kara da cewa, an kai shi asibiti amma lokitoci sun tabbatar da rasuwarsa, kuma tuni aka mika shi hannun danginsa.
- Hawan Jini: Gwamnatin Kano Ta Ci Alwashin Ci Gaba Da Yakar Cututtukan Dake Halaka Mutane
- Gwamna Abdulrazaq Ya Jajanta Wa Wadanda Hatsarin Jirgin Ruwan Gbajibo Ya Rutsa Da Su
wasu matasa dake zaune a unguwar sun dora alhakin hakan gwamnatoci sakamakon matsin rayuwar da ake ciki, da kuma rashin aikin yi da ya yi wa matasan katutu, inda suka ce da gwamnatotci suna yin abinda ya dace wajen tallafa matasan ba za a samu haka ba.
Sai dai sun yi kira ga matasan da suke yunkurin jefa kansu ga halaka da su daina su nemi na kansu don tsira da mutunci.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba mu samu ji daga bakin kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Harua Kiyawa ba.
Ba wanne ne karon farko ba, da ake samun mutuwar masu satar wayoyin wutar lantarki a lokacin da suke tsaka da aikata barna.