Yadda ƴan sanda suka gano ƙoƙon kawunan mutum 17 a Uganda

Spread the love

Ƴan sanda a Uganda sun zaƙulo ƙoƙon kan mutum 17 a gundumar Mpigi da ke tsakiyar ƙsar bayan da jama’a suka ankarar da su, kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito.

An gano ƙoƙon kawunan mutanen a wani waje da a baya ake amfani da shi a matsayin wurin bauta a ƙauyen Kapanga, in ji jaridar.

“Gano ƙoƙon kawunan ya zo ne bayan bayanan da suka samu daga mazauna garin da suka ce wasu yara biyu ne suka sanar da su abin da suka gani a lokacin da suka je neman ice a wurin ranar Lahadi.” in ji jaridar.

Ƴan sanda sun ce ana zargin wani mutum da ya tsere da ake nema ruwa a jallo da zama mamallakin wajen da aka yi aika-aikar.

A baya an yi kashe-kashe da ke da nasaba da ayyukan ƙungiyar asiri a Uganda har da kisan da aka yi a 2000 lokacin da aka ƙona ɗaruruwan mabiya addinin kirista.

Hukumomi sun tuhumi masu fafutuka 36 daga ɓangaren hamayya da ayyukan ta’addanci bayan da aka tusa ƙeyarsu daga Kenya mai maƙwabtaka.

Masu gabatar da ƙara sun zargi masu fafutukar da zuwa birnin Kisumu a yammacin Kenya cikin makon da ya gabata domin karɓar horon ta’addanci, zargin da jam’iyyar FDC mai hamayya ta musanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *