YADDA AKA GUDANAR DA HAWAN DAUSHEN SALLAH KARAMA A MASARAUTAR GAYA

Spread the love

A Ci Gaba da Gudanar da Shagulgulan Sallah Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulqadir a Wuni na biyu ya  Gudanar da hawan daushen sallah karama a yamma cin wannan Rana ta Alhamis 2 ga Watan Shawwal 1445A.H.

Mai Martaba Sarkin ya fito ne da Misalin Karfe Hudu da Minti Hamsin da Biyar, Sanye da Shiga ta alfarma bisa Hurden Doki,inda ya fita daga Gida ta kofar yamma yabi ta kofar kuka ya dawo ta kofar Kano.

Tare da Hakiman Masarautar ta Gaya Wanda Ya hada da Ciroman Gaya Farfesa Umar Ibrahim Abdulqadir,da Turakin Gaya Hakimin Dawakin Kudu,da Magajin Malam din Gaya,da Sarkin Dawaki Babba Na Gaya,da Sarkin Fadar Gaya,da Sarkin Tsaftar Gaya.

Sauran Sune ,Barayan Gaya,Dan Adalan Gaya,Dan Malikin Gaya,da Dan Darman din Gaya,da Sarkin Noman Gaya,da Makaman Gado da Masun Gaya,da Fagacin Gaya,da Bauran Gaya,da Sarkin Dawakin Tsakar Gida Na Gaya,Sarkin Shanun Gaya,da Yariman Gaya,da Magajin Garin Gaya,da Shattiman Gaya,da Dan Buran Gaya,da Dallatun Gaya,da Dan Goriban Gaya,da Wakilin Matawallen Gaya ,da Sauran Su.

A inda Garin Gaya yayi cikar kwari da Al’umma  wadanda suka zo daga ciki da Wajen Masarautar dan Kallon Hawan daushen.


Gwamnan jihar kano Injiniya. Abba Kabir Yusuf Wanda ya samu wakilcin Honorabil Shehu Wada Sagagi gami da rakiyar shugaban karamar Hukumar Gaya na riko Honorabil Abubakar jazuli Usman Gaya ,da Sauran ‘Yan Siyasa a Tawagar daban daban.

Sa Hannun
Jami’in Yada Labarai Na
Masarautar Gaya
Auwalu Musa Yola
11/4/2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *