Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja ta kama wasu mutum uku da ake zargi da fasa wani gida tare da sace zinare da wasu kayayyaki masu tsada a Abuja.
Bincike ya nuna cewa wanda ake zargi na farko yana sana’ar sayar da kifi a Kasuwar Kifi ta Kado da ke Abuja.
Sanarwar ta ce “waɗanda ake zargin sun yi wa gidaje uku fashi a unguwar Lugbe, kafin su shiga na huɗu sun yi amfani da wani ƙarfe wajen banƙara tagar gidan inda ta nan suka samu damar shiga gidan.
“Suna shiga gidan, kai-tsaye suka shiga binciken abin da za su uya sacewa.
“A lokacin da suke lalube, sai suka hangi wani akwati a ajiye, nan take suka ɗauka suka tafi da shi.
“Sun yi amfani da guduma wajen buɗe akwatin, inda suka samu kuɗi, takardu, da zinare a ciki.
Sai dai na farko da ake zargin, ya kira mai saye sannan ya sayar da kayan satar, kan kuɗi Naira miliyan 60,” a cewar sanarwar.
Rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike za ta miƙa su zuwa kotu domim girbar abin da suka aikta.