Yadda gobara ta ƙone wani coci ƙurmus a Legas

Spread the love

Wata gobara ta kone wata fitacciyar majami’a da ke Legas da aka fi sani da gidan David a lokacin da ma’aikata ke kokarin shirya wa wani taro.

Gobarar ta faru ne da safiyar jiya Laraba sa’oi kafin cocin ya soma wani taron shekara-shekara da yake samun halartar matasa da manya.

Wasu ma’aikata na aikin shirya dakin taron lokacin da suka gano wuta na tashi daga rufin ginin.

Dattawan Arewa da na Ibo sun yi alla-wadai da tafiye-tafiyen Tinubu

Me kaddamar da dakarun sa-kai da jihohin arewacin Najeriya ke yi ke nufi?

Wani shaida ya fada wa yan jarida cewa gobarar ta soma ne daga rufin ginin inda kuma ta gone wajen kurmus.

Shaidan ya ce a kan idonsu wutar ta kone kayan kide-kide da na’urarorin sanyi saboda ba za su iya yin komai ba saboda wutar da ke tashi gagga-gagga.

Sashen BBC Pidgin ya ruwaito yadda gobarar ta kone ginin baki daya inda yanzu ya zama toka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *