Wata hatsaniya da ta faru a yammacin ranar Talata a kasuwar Wuse da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta janyo ƙone-ƙonen shaguna da mutuwar wani matashi.
Lamarin ya faru ne bayan da jami’an kwamitin kula da tsarin kasuwa da masu sana’a suka kama mutanen da suka saɓa doka domin gurfanar da su a gaban kotu.
Wakilin BBC ya ruwaito cewa cikin mutanen da jami’an suka kama har da wani matashi da aka sa masa ankwa wanda ya yi yunƙurin guduwa sai dai jami’an sun bi shi tare da harbe shi.
Shugaban Bankin Duniya Ya Ziyarci Masarautar Gaya.
Ina nan Daram a Jam’iyar PDP: Atiku Abubakar
Lamarin dai ya fusata ƴan kasuwar da suka shiga zanga-zanga tare da farfasa motocin jami’an kwamitin.
Jami’an dai sun harba hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa mutanen da suke nuna fushinsu.
Wasu yan kasuwar da wakilinmu ya yi magana da su sun ce kashe matashin ne ya sa aka soma ƙone-ƙone lamarin da ya haddasa gobara.
Gobarar ta shafi shagunan sayar da atamfofi da labulai da zinare da jakunkunan mata.