Yadda kotu a Kano ta yanke wa mutum biyar hukuncin kisa bisa kisan wata mata kan zargin maita

Spread the love

Wata babbar kotu da ke jihar Kano ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya a jihar Kano, bayan da suka kashe wata mata wanda suka zarga da maita a shekara ta 2023.

Lamarin dai ya faru ne a ƙauyen Daɗin Kowa da ke ƙaramar hukumar Wudil ta jihar Kano.

Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun far wa Dahare Abubakar, mai shekara 67 lokacin da take aiki a gonarta, inda suka lakaɗa mata duka da kuma caka mata wuƙa har ta mutu.

Ƴan uwan matar ba su yi wata-wata ba suka garzaya wurin hukumomi – inda kuma aka cafke mutanen nan take a wani ƙauye mai nisan kilomita 45 daga birnin Kano.

Lamarin ya janyo hankula a faɗin ƙasar da kuma tayar da zazzafar muhawara kan yadda ake cigaba da kashe mutane a ƙauyuka da garuruwa bisa zargin maita.

Waɗanda suka yi zargin ba tare da wata hujja ba, sun yi imanin cewa waɗanda suka zarga ɗin na da hannu a mutuwar wani ɗan uwa ko janyo rashin lafiyarsa ko kuma rashin sa’arsa.

Da yake yanke hukunci, mai shari’a Usman Na’abba ya ce sun samu hujjoji ƙwarara kan mutanen biyar da ake zargi da kashe matar.

Lauyan masu shigar da ƙara, Abba Sorondinki, ya ce yana fatan hukuncin zai zama izina ga sauran mutane waɗanda ke ɗaukar doka a hannunsu da kuma yin zarge-zargen da ba su da tushe.

Kotun ta samu bayanai da ke cewa an kashe matar bayan da matar ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Abdulaziz Yahaya – wadda ba ta da lafiya – ta yi mafarkin cewa ta ga Dahare na bin ta riƙe da wuƙa.

Daga nan ne Yahaya ya ɗauki wasu mutane inda suka je suka fuskanci matar, abin da ya janyo mutuwarta.

“Akwai irin waɗannan lamura amma wannan shi ne karon farko da muke ganin an yanke wa mutum biyar hukuncin kisa bisa kashe wata da suka zarga da maita,” kamar yadda Sorondinki ya faɗa wa BBC.

Yaron matar, Musa Yahaya, ya ce ranar da aka kashe mahaifiyarsa ita ce tafi bakin ciki a rayuwarsa kuma ya ji daɗin hukuncin da aka yanke kan mutanen da suka kashe ta.

“Ina cikin farin ciki saboda su ma za su ɗanɗani abin da suka yi wa mahaifiyata,” in ji shi.

Lauyan da ke kare waɗanda ake zargi Ma’aruf Yakasai ya ce suna shirin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke.

So tari, ba kasafai ake aiwatar da hukuncin kisa a Najeriya ba kuma waɗanda ake yanke wa hukuncin kisa na kare rayuwarsu ne a gidan yari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *