Rahotanni daga jihar Kebbi da ake arewa maso yammcin Najeriya sun ce aƙalla mutum 15 ne suka mutu a wajen wani artabu tsakanin mutanen gari da mayaƙan nan ‘yan kasashen waje da ake kira Lakurawa.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Jumu’a a kusa da garin Mera na Karamar Hukumar Augie.
Jamilu Gulma wakilin jaridar Blueprint a jihar wanda ya bibiyi labarin ya shaida wa BBC cewa, wadansu makiyaye ne da suke kiwo a garin Mera, mutanen da ake sa ran ƴan Lukurawa ne suka ƙwace dabbobin.
“Sai makiyayin ya ruga da gudu ya shaidawa mutanen gari abin da ke faruwa, saboda haka matasan garin suka je aka yi artabu tsakanin su da mutanen a cikin jejin, inda aka kashe mutum 15 tare da jikkata wasu da dama.”
Jamilu Gulma ya ce mutanen garin sun yi nasarar kashe wasu daga cikin ƴanbindigar, tare da jikkata wasu da dama, sai dai sun dauke mutanensu.
“Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya kai ziyarar jaje a garin na Mera tare da kwamishinan yansanda da sauran jami’an tsaro da mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera.”
Ko a makon da ya gabata hukumomi da jama’a a jihar Sokoto da ke maƙwabtaka da jihar Kebbi, sun nuna damuwa kan ɓullar ƙungiyar Lakurarwan masu iƙirarin jihadi da ke gudanar da harkokinsu a wasu ƙananan hukumomin jihar biyar.
Mataimakin gwamnan jihar ta Sokoto, Alhaji Idris Muhammad Gobir, ne ya bayyana haka a yayin gabatar da wata maƙala a lokacin da ɗaliban kwalejin horon soja (Nigeria Defence College ) da ke Abuja suka kai wa jihar ziyara a ranar Juma’a da ta gabata.
Mataimakin gwamnan ya shaida wa BBC cewa ‘yan ƙungiyar waɗanda suke ɗauke da manyan makamai, suna yawo tare da wa’azi ga mazauna yankunan ƙananan hukumomin Tangaza da Gudu da Illela da Binji da kuma Silame.
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa ‘yan ƙungiyar sun shiga yankunan na Sokoto da jihar Kebbi ne daga ɓangaren yankin Sahel da ya ƙunshi ƙasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban na Sahel.
Sukan yi wa’azi tare da shaida wa jama’a cewa su ba su tare da ‘yansanda da sojoji, da ma duk wani jami’in gwamnati na siyasa kuma ba su yarda da karatun boko ba.
Masana harkokin tsaro na ganin cewa ɓullar wannan ƙungiya ba ƙaramar barazana ba ce ga ƙasar idan aka yi lakari da cewa wuri ne da fitacciyar kungiya mai iƙirarin jihadi a duniya take – Ansaru – kamar yadda Kabiru Adamu na kamfanin Beacon Consulting, mai bincike a kan harkokin tsaro a yankin Sahel ya shaida wa BBC.