Yadda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya sake komawa kan karaga

Spread the love

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ta 2024 bayan da majalisar dokoki ta soke dukkan masarautun jihar biyar da aka ƙirƙira a shekarar 2019.

Jim kaɗan bayan rattaba hannu a kan dokar, gwamnan ya sanar da naɗa Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano na 16, bayan ya sauke Aminu Ado Bayero daga kan kujerar.

Matakin kuma ya nuna cewa an soke masarautun Gaya da Bichi da Ƙaraye da kuma na Rano.

Shekaru huɗu da suka wuce ne gwamnan Kano na wancan lokacin, Abdullahi Umar Ganduje ya cire Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano bisa dalilan da suka haɗa da ‘rashin biyayya’ ga gwamnati.

Tun bayan da gwamnatin jam’iyyar APC ta sha kaye a zaɓen gwamna a 2023, lamarin da ya bai wa jam’iyyar NNPP damar kafa sabuwar gwamnati, masu sharhi suka soma bayanai a kan cewa Muhammadu Sanusi zai iya komawa kan kujerarsa.

Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin Khalifa Muhammadu Sanusi da kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na tsawo shekaru.

Kwankwaso ne ya naɗa Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 14 bayan rasuwar Alhaji Ado Bayero ƴan watanni bayan da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya cire Sanusi a matsayin gwamnan babban bankin ƙasar.

A farko shekarar 2024 ne maganar sake dawo da Sanusi kan karagar mulki ta soma fitowa fili bayan da Sanata Rabiu Kwankwaso ya tabbatar wa manema labarai cewa za a sake nazari a kan dokar da ta kafa sabbin masarautun Kano.

“Dole za a zo a yi magana, a duba a ga abin da ya kamata a yi a kai, gyara za a yi ko rusau za a yi,” in ji Kwankwaso.

Waɗansu masu sharhi sun ce tun lokacin kamfe, Sanusi ya nuna goyon bayansa ga Abba Kabir Yusuf kuma duk makusantar Khalifan Tijjaniyar sun goyi bayan jam’iyyar NNPP ta kafa mulki a jihar Kano.

Hakan ya sa masu sharhi da dama suke ganin cewa dama lokaci kawai ake jira domin a rama wa kura aniyarta.

‘Rama wa kura aniyarta’

Dr Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami’a ta CAS a Kano kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya ce akwai waɗanda za su iya ganin cewa alaƙar Sanusi da Kwankwaso ce ta sa aka mayar da shi kan mulki.

“Akwai waɗanda za su iya ganin hakan ta wani ɓangaren za a iya cewa haka ɗin ne, tun da buƙata ta haɗe a wuri ɗaya, sannan kuma duk an taimaka wa juna. Yanzu za a iya cewa wataƙila an tasamma yin haka ɗin ke nan ko kuma an tasamma rama wa kura aniyarta ne,” in ji Sufi.

Shin kana ga tafiyar za ta ɗore? Maganar da mutane da dama suke ta yi ke nan.

Sai Dr Kabiru Sufi ya ce “za ta iya ɗorewa kuma za ta iya samun matsala. Ya danganta ga abubuwan da suka biyo baya da kuma yadda dukkanin ɓangarorin suka karɓi al’amarin. Wannan hasashe ne da ba za a iya cewa ba. Wataƙila idan ɓangare ɗaya yayi haƙuri, to tafiyar za ta iya yin tsayi”.

“Amma kuma idan ya kasance aka samu akasin hakan, ya danganta da yadda ɓangarorin guda biyu ko kuma dukka waɗanda ke cikin al’amaran musamman sabuwar tafiya ɗin. Ya danganta ga yadda suka yi matsayin nasu shi ne zai sa a samu tsawo ɗin ko kuma a samu akasin hakan,” in ji Sufi.

Manyan dalilai uku da suka sa Ganduje ya cire Sanusi

A ranar tara ga watan Maris ɗin 2020 gwamnatin jihar Kano ta sanar da cire Muhammadu Sanusi II daga kan muƙaminsa na sarkin Kano.

Sanarwa da Sakataren Gwamnatin jihar na wancan lokacin Alhaji Usman Alhaji ya fitar ta ce ɗaukacin mambobin majalisar zartarwar jihar sun amince a cire Sarki Sanusi II.

  • Sukar Manufofin Gwamnati – Babban dalilin cire Sarki Sanusi II daga kan mulki shi ne sukar da yake yi wa manufofin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.
  • Rashin Biyayya – Sanarwar gwamnati a lokacin ta ce Sarkin Kano yana nuna rashin biyayya ga umarnin ofishin gwamna da na sauran hukumomin gwamnati, ciki har da rashin halartar tarukan da gwamnati ke gayyatarsa ba tare da bayar da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba.
  • Siyasa – Magoya bayan gwamnatin jihar Kano a wancan lokacin sun sha kokawa kan zargin da suke yi wa sarkin na shiga harkokin siyasa.

Wane ne Sarki Muhammadu Sanusi II ?

  • An haife shi a zuriyar sarakunan Fulani a ranar 31 ga watan Yuli 1961.
  • Jika ne ga Sarki Sanusi da aka sauke daga gadon sarauta.
  • Ya samu digiri a fannin tsimi da tanadi da fannin addini Musulunci.
  • An naɗa shi muƙamin gwamnan Babban Bankin Nigeria (CBN) a watan Yuni 2009.
  • Mujallar Banker ta bayyana shi a matsayin gwarzon shekara a 2010.
  • An dakatar da shi daga CBN a watan Fabrairu bayan ya samu saɓani da shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.
  • An naɗa shi a matsayin Sarkin Kano na 14 a ranar takwas ga watan Yunin 2014.
  • Sunansa ya canja daga Sanusi Lamido Sanusi zuwa Muhammad Sanusi II.
  • An sanar da shi a matsayin Khalifar Tijjaniya a Najeriya a watan Maris ɗin 2021.
  • Yana da mata huɗu da ƴaƴa da dama da kuma jikoki.

BBCH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *